Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da yin gaggawa da shirya jana'iza da yi mata sallah da kuma binneta; idan jana'izar ta kasance ta garice to alheri ne, kuke gabatarwa gare shi na ni'imar ƙabari, idan kuma ta kasance koma bayan haka ne to sharri ne kuke saukewa daga wuyayenku.