Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarci musulmai da ɗabi'u bakwai kuma ya hanesu ɗabi'u bakwai; waɗanda ya umarce su sune: Na farkonsu: Ziyarar mara lafiya. Na biyunsu: Raka jana'iza da tarayya ta hanyar yi mata sallah da kuma binneta, da yi mata addu'a. Na ukunsu: Yin addu'a ga wanda ya yi atishawa kuma ya godewa Allah, shi ne ace masa: Allah Ya yi maka rahama. Na huɗunsu: Kuɓutar da mai rantsuwa da kuma gasgata shi, ma'ana cewa da zai yi rantsuwa akan wani al'amari alhali kai kana da iko akan sanya shi kuɓutacce a cikinta to ka aikata; dan kada ka bar shi zuwa yin kaffara ta rantsuwar. Na biyarɗinsu: Taimakon wanda aka zalinta, ta hanyar taimaka masa da tunkuɗe abinda yake afka masa daga azzalimi gwargwadan iko. Na shidansu: Amsa gayyata zuwa walimar abin ci, kamar walimar angwanci, ko suna, ko waninsu. Na bakwansu: Yin sallama da yaɗata da kuma amsata. Waɗanda kuma ya hanasu su ne: Na farkonsu: Sanya zobunan zinare da kuma yin ado da su. Na biyunsu: Shan abu a ƙwaryar azirfa. Na ukunsu: Zama akan Mayasir, sune shimfiɗun da ake sawa akan sirdin doki da kuma sirdin raƙumi na alharaini. Na huɗunsu: Sanya tufafin da aka yi da kattanin da aka cakuɗa da alharini kuma ana ambatansa: (Alƙisiyyu). Na biyarɗinsu: Sanya alharaini. Na shidansu: Sanya Istabraƙ, shi ne: Alharini mai kauri. Na bakwansu: Sanya Dibaj, shi ne: Mafi kyan nau'ikan alharini kuma mafi tsadarsu.