explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kwaɗaitar da wanda ya zo masallaci ya shige shi a kowanne lokaci, da kowacce manufa, ya yi sallah raka'a biyu kafin ya zauna, su ne raka'o'i biyun gaisuwar masallaci.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • An so yin sallah raka'a biyu gaisuwa ga masallaci kafin zama.
  • Wannan umarni ne ga wanda ya yi nufin zama, wanda ya shiga masallaci ya fita kafin ya zauna umarnin bai shafe shi ba.
  • Idan mai sallah ya shiga (masallaci) alhali mutane suna cikin sallah, sai ya shiga cikinta tare da su, to, wannan ya wadatar masa daga raka'o'i biyun.