Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiryar da musulmi cewa idan ya yi nufin shiga masallaci ya yi wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - salati da faɗinsa: Ya Allah Ka yi tsira Ka yi aminci ga (Annabi) Muhammad, sannan ya ce: (Ya Allah Ka buɗe mini ƙofofin rahamarKa). Idan zai fita to ya yi wa Annabi salati sai ya ce: (Ya Allah Ka tsareni daga Shaiɗan abin jefewa). A cikin riwayar Hakim: Sai ya ce: (Ya Allah Ka tsareni daga Shaiɗan abin jefewa).