Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana halin hannaye a cikin sujjadar sallah, hakan da ya tabbatar da tafukansa a ƙasa kuma ya ɗora yatsun a ɗunƙule a fuskantar alƙibla, kuma gwiwowin hannaye - sune mararrabar zira'i da damutse - a ɗage daga taɓ ƙasa kuma a buɗe daga sasanni.