Salla dukkaninta girmama Allah ne ta hanyar zance da aiki, acikin wannan hadisin madaukaki akwai bayanin shiar na salla, shine tabbatar da girma ga Allah madaukaki, babban abin da ya kara nuna girmanta shi ne shar'anta ta da aka yi don girmama Allah da daukaka shi. A lokacin da masallaci zai fara salla sai ya yi kabbarar harama yana tsaye ya daidaita.bayan ya gama karatu ya tafi zuwa ruku'u,sai yayi kabbar, idan ya dago daga ruku'u, sai yace: Allah ya ji mai gode masa ,sai ya mike sosai sai ya godewa Allah ya yabe shi a tsayen,sai ya sake kabbara don kai goshi sujjada, sannan sai ya yi kabbara yayin da yake dago kansa daga sujjada,sai ya aikata haka a cikin dukkan salarsa, har ya kammala,idan ya mike don ciko raka'oi biyu bayan tahiya ta farko sa i ya yi kabbara yayin da yake mikewa. kuma shari'a ta sanya yin kabbara a kowane guri sai dai a waje dagowa daga ruku'u