Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi tafiya daga Makka zuwa Madina a tare da shi akwai sahabbansa, sai suka samu ruwa a hanyarsu, sai wasu daga sahabbai suka yi gaggawar alwala dan sallar La'asar har karshen kafafuwansu suka dinga bayyana ga mai kallo saboda bushewarsu daga ruwa, sai Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Azaba da halaka a cikin Wuta sun tabbata ga masu takaitawa a wanke karshen kafa a lokacin alwala, kuma ya umarcesu da sukai matuka a cikin cika alwala.