explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa mace auranta ba ya inganta sai da waliyyin da zai tsaya a ɗaurin auren.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Waliyyi sharaɗi ne a ingancin aure, idan aure ya faru ba tare da waliyyi ba, ko mace ta aurar da kanta, to, aurenta bai inagnta ba.
  • Waliyyi shi ne mafi kusancin mazaje ga mace, wani waliyyi na nesa ba zai aurar da ita ba, tare da samuwar waliyyi na kusa.
  • An sharɗanta (wasu) sharuɗɗa ga waliyyi: Ya zama mukallafi, kuma namiji, da shiriya a sanin maslahohin aure, da haɗuwar Addini tsakanin waliyyi da wanda zai yi wa walicci, duk wanda bai siffantu da waɗannan siffofin ba, to bai cancanci zama waliyyi a ɗaura aure ba.