Daurin Aure wani abu ne da yake da matukar hadari, yana halatta mafi tsadar abinda mace take kiyayewa, shi ne farjinta, kuma tana kasancewa sabida wannan Auren baiwa ga Mijinta, don haka sharia ta sanya mata Adalci da kuma jin kai da kuma Hikima kan ta zabi abokin zaman rayuwarta, kuma ta zabe shi da ganinta domin ita take son ta zauna da shi, kuma ita ce mafi sani da abinda tafi karkata da wanda take bukata. don haka Annabi don haka Annabi ya hana a aurar da bazawara har sai anji daga bakinta sannan kuma ta yarda, kamar yadda ya hana a aurara da Budurwa sai ta yadda ita ma kuma ta yi izinin hakan, kuma sabida cewa Budurwa tana da tsananin kunya sharia ta takaita da mafi saukin abu na daga Al'amarinta, kuma shi ne Izini, kamar yadda ta wadata da yin shirun ta kuma ya nuna yardar ta ne.