explain-icon

Bayani

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya tsawatar a kan jinkirta sallar La’asar daga lokacinta da gangan, kuma duk wanda ya yi hakan, to, aikinsa ya lalace, ya tafi kawai a watse.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Kwaɗaitarwa a kan kiyaye sallar la’asar a farkon lokacinta, da kuma gaggawar yinta.
  • Narkon azaba mai tsanani ga wanda ya bar sallar La’asar har loakcita ya fita, kuma barinta har fitar Lokacita ya fi tsanani a kan wata da ba ita ba, domin ita ce Sallah mafificiya wacce aka keɓance ta da umarni a faɗin Allah maɗaukaki: ((Ku kiyaye Salloli kuma ku kiyaye sallah mafificiya)). Bakara, 238.