Mafi yawan wasiyyar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga al'ummarsa ta kasance alhali shi yana cikin magagin mutuwa: Ku lazimci sallah ku kiyayeta, kada ku rafkana daga gareta, haka nan haƙƙoƙin abinda hannayenku suka mallaka na bayi maza da kuyangi mata ku kyautata mallakinsu, bai gushe ba yana maimaita ta, har maƙogwaransa ya fara gargarar mutuwa da ita, harshensa bai kusa ya bayyananar da ita ba.