Aisha tana bada labarin irin kaunar da Annabi tsira da amincin Allah ke yiwa asuwaki da kuma yadda ya damu da shi. Shi ne take fadar yadda Dan'uwanta - Allah ya yarda da shi- ya zo da danyen asuwaki wajen Annabi tsira da aminci su tabbata a gare shi lokacin barinsa duniyan. lokacin da Annabi tsira da aminci yaga asuwakin a wajensa, rashin lafiyarsa bata hana shi nuna yana son asuwakin ba, sai ya kalli asuwakin, kamar yana so, sai Aisha Allah ya yarda da ita ta kula da haka sai ta karbi asuwakin daga hannun Dan'uwanta ta sa bakinta ta gyarawa Annabi asuwakin, ta bashi ya goge bakinsa da shi -tsira da aminci su tabbata a gare shi. Aisha bata taba ganin wanda ya fi shi iya goge baki ba. Bayan ya gama goge bakin, sai ya daga yatsansa sama, yana dayanta Allah Madaukaki, sannan ya zabi komawa kusa da Mahaliccinsa, sannan ya rasu. Aisha tav kasance cikin farin ciki, ya cancanta tayi farin ciki kuwa, don kuwa Manzo tsira da amincin Allah ya rasu kansa na jingine a kirjinta.