Uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta bada labari game da wasu daga ɗabi'un Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, daga abinda ta ambata: Cewa shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba'a taɓa ba shi zaɓi ba tsakanin al'amura biyu sai ya ɗauki mafi sauƙinsu muddin dai mafi sauƙin ba mai kaiwa zuwa zunubi ba ne, to cewa shi zai kasance mafi nisantar mutane ga wannan zunubin kuma zai zaɓi mafi tsanani a lokacin. Kuma (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi bai taɓa ramuwa ba ga kansa a keɓance ba, kai ya kasance yana kau da kai kuma yana afuwa daga haƙƙinsa sai dai idan keta alfarmomin Allah aka yi sai ya zama ya yi hukunci saboda Allah, kuma ya kasance mafi tsananin mutane a fushi saboda Allah.