Sarkin muminai Usman ɗan Affan - Allah Ya yarda da shi - ya kasance idan ya tsaya akan wani ƙabari sai ya yi kuka har sai hawaye ya sa gemunsa ya yi dan shi, sai akace masa: Ana ambatan aljanna da wuta amma baka kuka dan shauƙi zuwa aljanna ko tsoron wuta! amma kana kuka saboda ƙabari? Sai ya ce: Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa ƙabari shi ne farkon masauki daga masaukan lahira, idan ya tsira ya kuɓuta daga cikinsa to abinda ke bayansa na masaukai su ne mafi sauƙi daga gare shi , idan bai tsira daga azabarsa ba; to abinda ke bayansa na uƙuba ya fi tsanani daga abinda ke cikinsa.