Abdullahi ɗan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ambaci cewa annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi bacci akan shimfiɗa ƙarama wacce aka saƙata da wasu daga tsirrai, sai ya miƙe alhali tabarmar ta yi tabo a fatar gefensa, sai muka ce: Ya manzon Allah, ina ma dai a ce mu yi maka wata shimfiɗa mai laushi da hakan ya fi kyau daga kwanciyarka akan wannan tabarmar mai kaushi, sai (annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Ni bana son sabo da duniya har in yi kwaɗayi a cikinta, kwatankwacina da wanzuwa a cikin duniya bai zama ba sai kamar wani matafiyi ne da ya sha inuwa ƙarƙashin wata bishiya sannan ya tafi ya barta.