Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa shi: Lokacin da aka hau da shi zuwa sama a daren Isra'i da Mi'iraji, ya wuce wasu mutane suna da farata na tagulla suna yakusa suna yayyaga fuskokinsu da ƙirazansu da su, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya tambayi (Mala’ika) Jibril - aminci ya tabbata agare shi -: Me waɗannan mutanen suka aikata har ake musu sakayya da wannan azabar? Sai (Mala’ika) Jibril - aminci ya tabbata agare shi - ya ce: Waɗanan sune waɗanda suke yi da mutane, kuma suke magana a kan mutuncinsu ba tare da gaskiya ba.