Huzaifa - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa su idan suka halarci abinci tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - basa sanya hannayensu a cikin abin cin har sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fara ya sanya hannunsa, cewa mu wani lokaci mun halarci abinci tare da shi, sai wata kuyanga (baiwa) ta zo saboda tsananin saurinta kai ka ce ana turota, sai ta tafi dan ta sanya hannunta a cikin abin cin, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya riƙe hannunta, sannan wani balaraben ƙauye ya zo kai ka ce ana turo shi ne, sai ya riƙe hannunsa kafin ya taɓa abin cin, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbat agare shi - ya ce: Lallai Shaiɗan yana samun dama a cikin abin ci idan ya fara cinsa ba tare da ambatan Allah - Maɗaukakin sarki - ba, lallai ya zo da wannan kuyangar ne dan ya halatta cin abin cin da ita sai na riƙe hannunta, sai ya zo da wannan balaraben ƙauyen dan ya halatta abin cin da shi, sai na riƙe hannunsa, na rantse da wanda raina yake a hannunsa, lallai hannun Shaiɗan yana hannuna tare da hannunta, sannnan ya ambaci sunan Allah ya ci.