Uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ambaci cewa wata mata miskiniya tana ɗauke da 'ya'yanta mata biyu sai ta tambayeta, sai ta bata dabinai uku, sai ta bawa kowacce daga cikin 'ya'yan nata mata biyu dabino ɗaya, kuma ta ɗaga ɗayan zuwa bakinta dan ta ci shi, sai 'ya'yan nata mata biyu suka nemi dabinon da take nufin cinsa, sai ta raba dabinon a tsakaninsu, sai lamarinta ya ƙayatar da Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita -, kuma ta faɗawa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - abinda matar ta aikata, sai ya ce: Lallai haƙiƙa Allah Ya tabbatar mata aljanna saboda wannan dabinon, ko kuma ya 'yantata daga wuta.