Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wata rana wani mutum yana tafiya a wata hanya, sai ya samu reshen wata ƙaya a kan hanyar, sai ya kawar da shi, sai Allah Ya yaba masa Ya kuma gafarta masa". Ingantacce ne - Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wata rana wani mutum yana tafiya sai ya wuce wani reshen bishiya a cikinsa akwai ƙayar da take cutar da musulmai, sai ya kawar da ita daga hanyar, sai Allah Ya yaba masa kuma Ya gafarta masa.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Falalar gusar da cuta akan hanya, kuma hakan sababi ne na (samun) gafarar Allah.
  • Rashin wulaƙantar da ayyukan alheri koda sun kasance kaɗan ne.
  • Musulunci addini ne na tsafta da kare yanayi da aminci na gaba daya.