explain-icon

Bayani

Ya kasance daga cikin karantarwar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ba ya ƙin karɓar turare, yana karɓarsa domin yana da sauƙin ɗauka, kuma yana da ƙamshi.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Mustahabbacin karɓar kyautar turare, domin babu wata wahala wurin ɗaukarsa, babu damuwa wurin karɓarshi
  • Cika da kyakkyawan halin Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi wurin ƙin karɓar turare da kuma karɓar kyauta daga wanda ya yi masa.
  • Kwaɗaitarwa a kan amfani da turare.