Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa mutane da a ce suna sanin abinda ke cikin kiran sallah da sahun farko na falala da alheri da albarka sannan ba za su samu damar samun shi ba sai sun yi ƙuri'a akan sa, waye a cikinsu ya fi cancanta akan ɗan uwansa ? da sun yi ƙuri'a, kuma da a ce suna sanin abinda ke cikin gaggawa zuwa sallah a farkon lokacinta da sun yi rigegeniya gareta, kuma da a ce suna sanin gwargwadan lada a zuwa sallar Issha'i da sallar Asuba da zuwa gare su ya yi sauƙi koda da jan ciki ne akan gwiwowi kamar yadda yaro yake tafiya a farkon al'amarinsa.