Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya gargaɗar daga wucewa ta gaban wanda yake sallar farilla ko nafila, kuma cewa da wanda yake aikata haka da gangan da ya san abinda zai haɗu da shi na laifi; da a ce ya zaɓi ya tsaya arba'in; to shi ne mafi alheri gare shi da ya wuce ta gabansa. Abu al-Nadhr maruwaicin hadisin ya ce: Ban sani ba ya ce kwanaki arba'in ne ko wata ko shekara.