Annabi -tsira da aminci su tabbata a gare shi- ya umarci masu raba gado da su raba wa waɗanda suka cancanci rabon bisa adalci kamar yadda sharia ta yi bayani, kamar yadda Allah Yake nufi, sai a baiwa magada abin da Allah ya kaddarawa kowa a cikin Littafinsa, shi ne biyu cikin uku, da ɗaya cikin uku, da ɗaya cikin shida, da Rabi, da ɗaya cikin huɗu, da ɗaya cikin takwas. Abin da ya yi saura bayan wannan, to sai a baiwa mafi kusanci ga mamacin daga cikin maza; su ake kira Asubai.