Wasu mutane daga ƙabilu biyu na Ukl da Urainah waɗanda su musulmai ne sun zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai wata cuta ta samesu wacce cikinsu ya kumbura, kuma suka ƙyamaci zama a Madina saboda abincinta da iskarta ba su dace da su ba. Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarcesu su je inda raƙuman zakka suke, su sha fitsarinsu da nononsu, sai suka tafi, lokacin da suka samu lafiya suka yi ƙiba launinsu ya dawo musu sai suka kashe mai kiwon dabbobin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, suka kora raƙuman, sai labari ya zo a farkon yini (da safe), sai ya aika a nemo su, sai aka riskesu, lokacin da rana ta ɗaga sai aka zo da su gurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a ɗaure, sai ya yi umarni a yanke hannayensu da ƙafafuwansu, kuma aka tsiyayar da idanuwansu, domin haka suka yi wa makiyayin, kuma aka jefasu a cikin zafin rana, sunan neman a shayar da su ruwa amma ba'a shayar da su, har suka mutu. Abu Ƙilabah ya ce: Lallai su sun yi sata, sun yi kisa, sun kafirce bayan sun yi imani, kuma sun yaƙi Allah da ManzonSa.