Daga Ikramah: Cewa Aliyu - Allah Ya yarda da shi - ya ƙona wasu mutane, sai labarin ya kaiwa Ibnu Abbas sai ya ce: Da ace ni ne ba zan ƙonasu ba; domin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Kada Ku yi azaba da azabar Allah», da na kashe su kamar yadda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Duk wanda ya canja Addininsa to ku kashe shi». Ingantacce ne - Bukhari ne ya rawaito shi
explain-icon

Bayani

Aliyu ibnu Abi Ɗalib - Allah Ya yarda da shi - ya yi ijtihadi sai ya ƙona wasu mutane daga cikin zindiƙai waɗanda suka yi ridda suka bar Musulunci (ya Kona su) da wuta, sai labarin hakan ya kai ga Abdullahi ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su -, sai ya ƙarfafe shi akan kisan su; sai dai ya yi inkarin ƙona su da wuta. Kuma ya ce: Da ace nine a matsayinsa da ban ƙonasu da wuta ba; domin shi Annabi- tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa babu mai yin azaba da wuta sai Ubangijin wuta, saidai kashesu ya wadatar, inda (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Duk wanda ya yi ridda daga Musulunci ya canja Addinisa zuwa wani Addinin daban to ku kashe shi.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Wajabcin kashe wanda ya yi ridda ya bar Musulunci da ijma'in ma'abota ilimi, hakan da sharuɗɗansa, bamai aikata haka sai shugaba da alƙali.
  • Faɗinsa: "Wanda ya canja Addininsa to ku kashe shi" wato: Wanda ya yi ridda daga Musulunci: Hukunci ne gamamme ga maza da mata.
  • Wanda ya yi ridda ba'a barinsa akan riddarsa, kai za'a kira shi zuwa ga Musulunci, idan bai amsa ba sai a kashe shi.
  • A cikin wannan hadisin akwai hani akan azabtarwa da wuta, kuma haddodi ba'a zartar da su da wuta.
  • Falalar Ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su -, da yalwar iliminsa da fahimtarsa da hadisan Annbi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
  • A cikin wannan akwai ladabin inkari akan wanda ya saɓa.
explain-icon

kashe kashe

explain-icon

Kari