Abdullahi Ibnu Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ambaci cewa su sun kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a wata tafiya, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tafi dan wata buƙatarsa, sai sahabbansa suka samu wata tsuntsuwa tare da 'ya'yanta biyu, sai suka ɗaukesu, sai tsuntsuwar ta fara fakan-fakan da fukafukanta tana buɗesu dan firgicin rasa 'ya'yanta, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kuma ya ce: Waye ya baƙanta mata rai ya tsoratar da ita ta hanyar ɗauke mata 'ya'yanta?! Sannan ya yi umarni a mayar mata da su. Sannan ya ga wani ramin tururuwar da aka ƙona shi da wuta, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Waye ya ƙona wannan? Wasu daga cikin sahabbansa suka ce: Mu ne. Sai ya ce da su: Lallai ba ya halatta ga wani ya azabtar da mai rai da wuta; sai Allah Mahaliccinta.