Wani balaraben ƙauye ya shiga cikin masallacin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a ranar Juma'a ta ƙofar da ke kudancin masallaci daura da gidan Umar ɗan Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi -, alhali Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana tsaye yana huɗuba, sai mutumin ya fuskanci Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, kuma ya ce: Ya Manzon Allah, dabbobi sun halaka, hanyoyi sun yanke saboda mutuwar dabbobin da suke ɗaukar mutane ko sun yi rauni saboda yunwa, to ka roƙa mana Allah Ya shayar da mu ruwa. Sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ɗaga hannayensa, sannan ya ce: Ya Allah Ka shayar da mu, ya Allah Ka shayar da mu, ya Allah Ka shayar da mu. Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wallahi ba ma ganin ko da wani yanki na girgije daga sama, kuma tsakaninmu a cikin masallaci da dutsen Sal'a a yammacin masallaci inda ta ɓangarensa ne girgijen ya zo babu wani ɗaki ko gida da zai karesu daga ganinsa. Anas - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Sai wani kewayayyen girgije kwatankwacin garkuwa ya ɓullo shi ne ƙaramin faranti, lokacin da ya tsaya a tsakiyar saman Madina sai ya yaɗu, sannan ya zubar da ruwa, na rantse da Allah, bamu ga rana ba saboda ruwan har wata Juma'ar daban, inda wancan mutumin ya shiga ta waccar ƙofar, alhali shi tsira da amincin Allah su tabbata agare shi yana tsaye yana huɗuba, sai ya fuskance shi yana tsaye, sai ya ce: Ya Manzon Allah, dukiyoyi sun halaka, hanyoyi sun yanke, to ka roƙa mana Allah Ya ɗauke mana ruwan. Ya ce: Sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ɗaga hannayensa, sannan ya ce: Ya Allah Ka juyar da ruwan a gefanmu ba'a kanmu ba, ya Allah akan abin da ya ɗago daga ƙasa kamar tudu, da ƙaramin dutse, da cikkunan kwari, da matsirar bishiyoyi (jijiyoyin bishiya). Anas ya ce: Sai girgijen da yake zubar da ruwan ya yanke, sai muka fita muna tafiya cikin rana.