Allah yana Jarrabar bayinsa da nau'o'i na Bala'i; don su rokeshi shi kadai kuma suyi ta ambatonsa, to yayain da akayi fari a lokacin Annabi ya futo filin Idi a sahara; don ya nemi shayarwa daga Allah, kuma wannan shine yake nuna kaskantar da kai ga Allah, sai ya fuskanci Alkibla, don fatan amsa Addua, kuma ya fara rokon Allah kuma yana neman agajinsa ga Musulmi, kuma ya gusar musu da abinda ya ke damunsu na fari, da kwadayin canza musu daga halin fari zuwa na Ni'ama, daga halin Matsuwa zuwa halin yalwa, sai ya juya gwadonsa izuwa daya bangaren, sannan kuma yayi musu Sallar Rokon ruwa raka'a biyu, kuma ya bayyana karatu a cikinsu; domin irinsu daya da Sallar Jumu'a.