Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa wanda ya yi alwala sai ya kyautata alwalarsa da cikawa da zuwa da sunnoninta da ladubbanta, sannan ya zo sallar Juma'a kuma ya yi shiru ya karkata ga mai huɗuba, kuma ya yi shiru daga yashasshiyar magana; za'a gafarta masa ƙananan zunuban kwana goma, daga sallar Juma'a zuwa Juma'a ta biyu da ƙarin kwanuka uku; domin kyakkyawa da kwatankwacinta goma. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya gargaɗar daga rashin fuskantar zuciya ga abinda ake faɗa a cikin huɗuba na wa'azuzzuka, da kuma wasa da gabbai na shafar tsakwankwani da waninsu na nau’ukan wasa da shagaltuwa, cewa wanda ya aikata hakan to haƙiƙa ya yi yashasshiyar magana, wanda ya yi yashasshiyar magana to ba shi da rabo a cikin ladan Juma'a cikakkiya.