explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da barin abin da kake kokwanto akansa na maganganu da ayyuka cewa shin an hana kuwa ko a'a, shin haramun ne ko halal ne, zuwa ga abin da baka kokwanto a cikinsa daga abin da ka tabbatar da kyawunsa da kuma halaccinsa.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Ya wajaba akan musulmi ya gina al'amuransa akan yaƙini da barin abinda ake kokwanto a cikinsa, kuma ya zama mai basira akan Addininsa.
  • Hani daga afkawa cikin shubuhohi.
  • Idan kana son nutsuwa da hutu to kabar abinda ake kokwanto a cikinsa ka jefar da shi a gefe.
  • Rahamar Allah ga bayinSa, dan Ya umarcesu da abinda a cikinsa akwai hutun rai da zuciya, kuma ya hanesu daga abinda a cikinsa akwai raurawar zuciya da kuma ɗimuwa.