Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa wani musulmi ba zai suturta ɗan uwansa musulmi ba a cikin wani al'amari daga al'amura, sai Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya suturta shi a ranar alƙiyama; sakayya tana daga jinsin aiki, kuma suturcewar Allah gare shi zai zama da suturcewar laifukansa da saɓonsa daga yaɗasu ga ma'abota taron alƙiyama, zai iya kasancewa da barin yi masa hisabi akansu da kuma anbata masa su.