explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa son mutanen Ansar daga mutanen Madina, alama ce akan cikar imani; wannan dan rigayarsu a taimakon Musulunci da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, da kokari akan tarbar musulmai, da bada dukiyoyinsu da rayukansu a tafarkin Allah, kuma cewa kinsu alama ce ta munafunci. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya bayyana cewa wanda ya so mutanen Madina Allah Zai so shi, wanda ya ki su Allah Zai ki shi.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • A cikinsa akwai daraja mai girma ga mutanen Madina, son su alamce akan imani da kubuta daga munafunci.
  • Son masoya Allah da taimakonsu sababine na samun son Allah ga bawa.
  • Falalar wadanda suka rigaya na farko a cikin Musulunci.