Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa sahabbansa wa'azi wa'azi isasshe zukata sun ji tsoro daga gare shi, kuma idanuwa sun zubar da hawaye daga gare shi, Sai suka ce : Ya Manzon Allah ! kai ka ce wannan wa'azin bankwana ne, saboda abinda suka gani ya kai matukarsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a wa'azi, sai suka nemi wata wasiyyar dan su yi riko da ita a bayansa, Ya ce: Ina yi muku wasicci da tsoron Allah - Mai girma da daukaka -, hakan da aikata wajibai da barin abubuwan da aka haramta, da ji da bi, wato: Ga shugabanni, koda bawa ne ya shugabanceku ko ya yi rinjaye a kanku, wato ya zama mafi kaskantar halitta sarki akanku kada ku hanu daga hakan, ku bi shi dan tsoron tada fitintinu, domin shi wanda ya rayu daga cikinku zai ga sabani mai yawa. Sannan ya bayyana musu mafita daga wannan sabanin, hakan dayin riko da sunnarsa da sunnar Halifofi shiryayyu a bayansa, Abu bakar Al-Siddik, da Umar Dan Al-khaddab, da Usman Dan Affan, da Aliyu Dan Abu Dalib - Allah Ya yarda su baki daya -, da riketa da turamen hakora wato - turamen hakora na karshe -: Yana nufi da hakan kokari a lazimtar sunna da yin riko da ita, ya kuma gargadesu daga fararrun al'amura kirkirarru a Addini, domin cewa kowacce bidi'a bata ce.