Annabi SAW yayi bayanin cewa biyayya gare shi tana daga cikin biyayya ga Allah, kuma Annabi SAW baya Umarni sai da Shari'a wacce Allah ya Shar'anta ga Al'ummarsa to idan yai Umarni da da wani abu to shi Sharia ne kuma duk wanda ya bi shi to ya bi Allah, kuma duk wanda ya saba Masa to ya sabawa Allah, kuma Shugaba idan Mutum ya bi shi to hakika ya bi Manzo SAW kuma idan ya Saba masa to hakika ya sabawa Manzon; domin Annabi SAW shi wanda ya yi umarni da hakan a cikin mafi yawan Hadisai; sai dai in yayi Umarni da Sabo