Daga Zainab 'yar Jahsh - Allah Ya yarda da ita - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiga gurinta a firgice yana cewa; "Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, azaba ta tabbata ga larabawa daga sharrin da ya kusanto, a yau an buɗe katangar Yajuju da Majuju kwatankwacin hakan" sai ya kewaye ɗan yatsansa babba da wanda yake biye da shi. Zainab 'yar Jahsh ta ce : Sai na ce ya Manzon Allah: Shin zamu halaka alhali a cikinmu akwai salihai? ya ce: "Eh, idan barna ta yi yawa". Ingantacce ne - Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiga gurin Zainab 'yar Jahsh - Allah Ya yarda da ita - a firgice a tsorace, alhali shi yana cewa: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, dan sanarwa da tinanin afkuwar wani al'amari abin ki da zai faru, kuma babu tsira daga gare shi sai fakewa ga Allah - tsarki ya tabbatar maSa -, sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Kaico ya tabbata ga Larabawa daga wani sharrin da afkuwarsa ya kusanto, yau an buɗe katangar Yajuju da Majuju, shi ne katangar da Zulkarnaini ya ginata, misalin wannan; sai ya kewaye ɗan yatsansa babba da wanda ke biye da shi. Sai Zainab - Allah Ya yarda da ita - ta ce : Yaya Allah Zai halakar da mu alhali a cikinmu akwai muminai na gari? Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce mata: Idan barna ta yi yawa da fasikanci da fajirci da sabo, da zina, da giya, da wasunsu, to halaka zata game kowa da kowa.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Firgici ba ya shagaltar da mumini daga ambatan Allah a lokacin tsoro; domin da ambatan Allah ne zukata suke nutsuwa.
  • Kwaɗaitarwa akan hana sabo da hana afkuwarsa.
  • Halaka mai gamewa tana faruwa saboda sababin yawan sabo da yaɗuwarsa da rashin hanawa koda mutanen kirki sun yawaita.
  • Masifu suna game mutane baki ɗaya salihai da batattu, saidai za’a tashe su ne akan niyyoyinsu.
  • Ya kebanci Larabawa a cikin faɗinsa: "Kaico ya tabbata ga Larabawa daga wani sharrin da ya kusanto"; domin su ne mafi yawan waɗanada suka musulunta lokacin da ya faɗi hakan.