Wani mutum daga cikin Yahudawa ya zo gurin sarkin muminai Umar - Allah Ya yarda da shi - kuma ya ce masa: Wata aya ce da kuke karantata a cikin littafinku Alƙur'ani, da ace mu jama'ar Yahudawa ne ta sauka a garemu a cikin littafinmu Attaura da mun maida wannar ranar idin da zamu dinga taruwa da shi; dan godiya ga ni'imar saukar wannan ayar mai girma, sai Umar - Allah Ya yardada shi - yace masa: Wace aya ce? Ya ce: {Kuma yaune Na cika muku Addininku, kuma Na cika muku ni'imaTa kuma Na yarje muku musulunci a matsayin Addini} Sai Umar - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Haƙiƙa mun san wannan ranar, da gurin da ayar mai girma ta sauka a cikinsa, haƙiƙa ta saukane ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -a ranar idi, ita ce ranar Juma'a alhali shi yana tsaye a Arfa, kuma su ranaku biyu ne masu girma a wurin musulmai.