explain-icon

شیکردنەوە

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana alwala a kowacce sallar farilla ko da alwalarsa ba ta karye ba, hakan don tabbatar da lada da kuma falala. Ya halatta ya sallaci sama da sallah (ɗaya) da alwala ɗaya muddin dai yana da alwala.

explain-icon

لە سوودەکانی فەرموودەکە

  • Mafi yawancin aikin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - shi ne yin alwala ga kowace sallah; don neman mafi cika.
  • An so yin alwala a lokacin kowace sallah.
  • Halaccin yin sama da sallah (ɗaya) da alwala ɗaya.