Daga Abu Hazim ya ce: Na zauna da Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - shekara biyar, sai na ji shi yana zantarwa daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ya ce; "Banu Isra'il sun kasance Annabawa ne suke shugabantarsu, duk lokacin da wani Annabi ya rasu sai wani Annabin ya maye gurbinsa, lallai cewa babu wani Annabi a baya na, za'a samu halifofi zasu yawaita" Suka ce: Da me zaka umarce mu? ya ce: "Ku cika caffar na farko sai na farko, ku basu haƙƙinsu, domin cewa Allah Mai tambayarsu ne daga abinda Ya basu kiwo". Ingantacce ne - Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Banu Isra'il sun kasance Annabawa ne suke shugabantar su, suna jiɓintar al'amuransu kamar yadda sarakuna da shugabanni suke aikatawa da talakawansu, a duk lokacin da ɓarna ta bayyana a cikinsu sai Allah Ya aiko musu da wani Annabin da zai daidaita al'amarinsu kuma ya gusar da abinda suka canja na hukunce-hukunce. Lallai cewa babu wani Annabi a bayana (ballantana) ya aikata abinda waɗancan suke aikatawa, za'a samu halifofi a bayana zasu yawaita kuma jayayya da saɓani zasu faru a tsakaninsu. Sai sahabbai - Allah Ya yarda da su - suka tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Da me zaka umarce mu? Sai ya ce: Idan Aka yi wa halifa caffa bayan wani halifan; to caffar na farko ce ingantacciya wajibine a cikata, caffar na biyun kuma ɓatacciya ce kuma nemanta yana haramta, kuma ku basu haƙƙinsu, ku bisu ku yi mu'amala da su da ji da bi inba a saɓon ba ne, domin cewa Allah Zai tambayesu kuma Zai yi musu hisabi a kan abinda suke aikata shi gareku.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Babu makawa ga talakawa daga wani Annabi ko halifa da zai tsayu da al'amarinsu, kuma zai ɗorasu akan hanya madaidaiciya.
  • Cewa babu wani Annabi bayan Annabinmu Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
  • Gargaɗarwa daga fito na fito akan wanda shugabancinsa ya tabbata ta hanya ta shari'a.
  • Ba ya halatta a yi caffa ga halifofi biyu a lokaci ɗaya.
  • Girman nauyin shugaba, domin cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Zai yi masa hisabi game da talakawansa.
  • Ibnu Hajar ya ce: Gabatar da al'amarin Addini akan al'amarin duniya; domin cewa shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da cika haƙƙin shugaba dan abinda ke cikinsa na ɗaukaka kalmar Addini da kame fitina da sharri; da jinkirta al'amarin nema da haƙƙinsa ba zai sarayar da shi ba, haƙiƙa Allah Ya yi masa alƙawari cewa Shi Zai tseratar da shi kuma zai cika masa koda a gidan lahira ne.
  • Alama ce daga alamomin Annabcinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, haƙiƙa halifofi sun yawaita a bayansa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, kuma masu gyarawa da masu munanawa sun jerantu ga al'umma.