Uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta bada labarin cewa farkon abinda aka farawa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da shi na wahayi shi ne mafarki na gaskiya a cikin bacci, ya kasance ba ya ganin mafarki sai ya hakan ya zo a bayyane mai kama da hasken Asuba, sannan aka sa masa son kaɗaitaka, ya kasance yana kaɗaitaka a kogon Hira sai ya yi bauta a cikin wasu 'yan darare ƙididdigaggu kafin ya koma ga iyalinsa, kuma ya tafi da guzuri saboda hakan, sannan ya dawo gurin Uwar muminai Nana Khadija - Allah Ya yarda da ita - sai ya yi guziri ga kwatankwacin adadin dararen, har sai da umarni na gaskiya ya zo masa alhali shi yana kogon Hira. Sai Mala'ika Jibril - aminci ya tabbata agare shi - ya zo masa sai ya ce masa: Ka yi karatu, sai (Manzo) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Ban iya karatu ba, ya ce: Sai ya kamani ya damƙeni ya matseni har sai da yakaini ƙololuwa a wahala sannan ya sakeni, sai ya ce: Ka yi karatu, nace: Ban iya karatu ba, sai ya kamani ya damƙeni karo na biyu har sai da yakai ƙololuwa a wahalar da ni sannan ya sakeni, sai ya ce: Ka yi karatu, sai na ce: Ban iya karatu ba, sai ya kamani a karo na uku sai ya damƙeni karo na uku sannan ya sakeni, sai ya ce: {Ka yi karatu da sunan Ubangijinka wanda Ya yi halitta. Ya halicci mutum daga gudan jini. Ka yi karatu alhali Ubangijinka Shi ne Mafi gima}. [al-Alaƙ: 1-3]. Sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya dawo da ayoyin zuciyarsa tana karkarwa dan jin tsoron mutuwa, sai ya shiga wurin matarsa Uwar muminai Nana Khadija 'yar Khuwailid - Allah ya yarda da ita -, sai ya ce: ki lulluɓeni da tufafi, sai suka lulluɓe shi da tufafi har sai da tsoron ya tafi daga gare shi, sai ya faɗawa Nana Khadija kuma ya bata labari, kuma ya ce: Haƙiƙa na ji wa kaina tsoron mutuwa, sai Nana Khadija ta ce: A'a, wallahi har abada Allah ba zai kunyataka ba, lallai kai kana sadar da zumunci, kana ɗaukar nauyin mai rauni wanda ba zai iya tsayuwa da kansa ba, kana bawa talaka wanda ba shi da komai; inda kake baiwa mutane abinda ba za su same shi ba a wurin waninka ba, kuma kana tarbar baƙi, kuma kana taimako akan masifu na gaskiya. Sai Nana Khadija ta tafi da shi har kai shi wurin Waraƙah ɗan Naufal ɗan Asad ɗan Abdul'uzza, shi ɗan kawunta ne, kuma ya kasance mutum ne da ya bar jahiliyya ya kasance kirista, ya kasance yana rubuta abinda Allah Ya so ya rubuta na Injila da harshen Ibraniyanci, kuma ya kasance dattijo ne mai yawan shekaru, ba ya gani, sai Nana Khadija ta ce da shi: Ya kai ɗan kawu, ka ji daga ɗan ɗan'uwanka, sai Waraƙah ya ce masa: Yakai ɗan ɗan'uwana, me kake gani? Sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ba shi labarin abinda ya gani, sai Waraƙah ya ce masa: Wannan Jibril ne wanda Allah Ya saukar da shi ga AnnabinSa Musa - aminci ya tabbata agare shi -, kaicona a ce ni matashi ne ƙaƙƙarfa a cikinsu (kwanukan da za'a aikoka), inama dai a ce zan zama ina raye lokacin da mutanenka zasu koreka, sai (Manzo) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Shin su zasu koreni?! Ya ce: Eh, babu wani mutum da ya zo da abinda ka zo da shi ba sai an cutar da shi, idan lokacinka ya riskeni zan taimakeka taimako mai ƙarfi. Sannan Waraƙah bai rayu tsawon lokaci ba sai ya rasu, kuma wahayi ya yi jinkiri tsawon lokaci.