Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labari alhali shi yana bada labari game da tsayawar wahayi da kuma dakatar da saukarsa a farkon manzancinsa: Wata rana ina tafiya a lungun Makka sai na ji wata ƙara daga sama sai na ɗaga idona, sai ga mala'ikan da ya zo mini a kogon Hira yana zaune akan kujera tsakanin sama da ƙasa, sai na tsorata na razana daga gare shi, sai na dawowa iyalina sai na ce: Ku lulluɓeni da tufafi. Sai Allah - Maɗaukakin sarki - Ya saukar da: {Ya kai mai lulluɓa} mai lulluɓa da tufansa, {Ka ta shi} da kira {Ka yi gargaɗi} ka gargaɗar da wanda bai yi imani da saƙonka ba. {Ubangijinka} Ubangijinka abin bauta {Ka girmama} ka gode maSa ka girmamaShi. {Tufafinka} tufafinka {Ka tsarkake} ka tsamosu daga najasa, {Gumaka} da bautar gumaka da mutun mutumi {To ka ƙaurace} ka bari, sai wahayi ya yi ƙarfi bayan haka ya yi yawa.