An tambayi Uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - game da ɗabi'un Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ta ce: Alfasha da munanan maganganu ko ayyuka ba su zama daga ɗabi'unsa ba, kuma ba ya ɗorawa kansa alfasha, kuma ba ya yi da gangan, kuma ba ya ihu yana ɗaga muryarsa a cikin kasuwanni, kuma ba ya rama mummuna da mummuna, sai dai yana sakayya da kyakkyawa, kuma yana yin afuwa a baɗini, kuma yana kau da kai yana kawar dakai a zahiri.