explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya cewa Munzir ibnu A'iz ga mai tabo a fuskar nan na ƙabilar Abdulƙais kuma shugabanta - Allah Ya yarda da shi - Lallai kai kana da siffofi biyu Allah Yana sonsu, sune: Hankali, da kuma tabbata da nutsuwa da kuma rashin gaggawa.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Kwaɗaitarwa akan ɗabi'antuwa da haƙuri da kuma dangana.
  • Kwaɗaitarwa akan tabbata a cikin al'amura da kuma duba ƙarshensu.
  • Haƙuri da dangana suna daga cikin siffofi ababen yabo.
  • Mutum ya godewa Allah - Maɗaukakin sarki - akan abinda Ya halicce shi akansa na ɗabi'u ababen yabo.
  • Kalmar al-Ashaj ita ce wanda aka jiwa rauni a fuska, ko a kai, ko goshi.