Annabi - tsira da amincin Allah su tabbat agare shi - ya bayyana cewa yana daga mafi soyuwarku gare shi a duniya, kuma mafi kusancinku mazauni da shi a ranar Alkiyama (su ne) mafi kyawunku a ɗabi'u, kuma cikin mafi ƙiyayyarku gare shi a duniya, kuma mafi nisantarku mazauni daga gare shi a ranar Alkiyama masu munanan ɗabi'u a cikinku; (masu yawan surutu) sune masu yawaita magana dan ɗorawa kai da kuma fita daga gaskiya, (masu tsanantawa kuwa) sune masu yalwatawa a cikin zance dan ɗorawa kai fasaha da girmama maganarsu ba tare da kiyayewa ba, (da masu girman kai). suka ce: Ya Manzon Allah, haƙiƙa mun san masu yawan surutu da masu tsanatwa, to su waye masu jiji da kai? Ya ce: masu girman kai masu yi wa mutane izgili wadanda suke yawaita magana kuma suke bude bakunansu da shi.