Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana cewa a lokacin tsananin baƙin ciki da takaici gareshi: "Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah" babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, "Mai girman" daraja, mai girman sha'ani, a cikin zatinSa da siffofinSa da ayyukanSa, "Mai haƙuri" wanda ba Ya gaggauto da uƙuba ga mai saɓo kai Yana jinkirtata, kuma Zai iya yi masa afuwa tare da iko akansa, Shi ne Mai iko - tsarki ya tabbatar maSa akan kowane abu. "Babu abin bautawa da gaskiya sai Ubangijin al'arshi mai girma" Mahaliccin al'arshi Mai girma. "Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Ubangijin sammai da ƙasa" kuma Mahaliccin sammai da ƙasa, kuma Mahaliccin kowane abu a cikinsu kuma Mamallakinsa kuma Mai gyara shi , kuma Mai tasarrufi a cikinsa yanda ya so, "Ubangijin al'arshi mai girma" Mahaliccin al'arshi mai girma.