Baffan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - Abbas ɗan Abdulmuɗɗalib - Allah Ya yarda da shi - ya nema daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya sanar da shi addu'ar da zai roƙi Allah ita, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya sanar da shi cewa ya roƙi Allah lafiya da kuɓuta daga illoli da aibuka a addini da duniya da lahira, Abbas ya ce: Bayan wasu kwanuka sai na dawo zuwa gare shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - karo na gaba ina tambayarsa ya sanar dani addu'ar da zan nemeta daga Allah, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce masa yana mai nuna masa kauna: Ya Abbas, ya baffan Manzon Allah, ka roki Allah lafiya dan tunkude kowace cuta da jawo kowane alheri da anfani a duniya da lahira.