explain-icon

Bayani

Ma’aikin tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana ba da labarin cewa duk wanda a rana ya faɗa sau ɗari: Tsarki ya tabbata ga Allah haɗi da gode masa. an share kurakuransa an kuma gafarta su, ko da suna da yawa misalin farar kunfar nan ce da take saman teku lokacin kaɗawar igiya da ambaliya.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Wannan ladan yana samuwa ne ga wanda ya faɗeta a rana a jere ko a rarrabe.
  • Tasbihi: Tsarkake Allah daga tawaya. Godiya: Siffanta Allah da cika tare da so da kuma girmamawa.
  • Abin nufi da Hadisin kankare ƙananan zunubai, amma manyan dole sai da an tuba.