Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya aika Mu'az ibnu Jabal - Allah Ya yarda da shi - zuwa Yaman dan koyar da mutane da kuma kiransu, daga cikin abin da ya umarce shi da shi shine ya karɓi Zakkar shanunsu tabi'i ɗaya namiji ko mace daga dukkanin talatin; shine wanda ya cika shekara ɗaya, haka (ya karɓi) Musinna daga dukkanin arba'in; ita ce wacce ta cika shekara biyu. Kuma ya karɓi jizyar dinari ɗaya daga mazowa littafi Yahudawa da Nasara daga dukkanin namiji baligi, ko abin da ya yi daidai da dinari ɗaya na tufafin Yaman waɗanda ake kiransu da: Ma'afirri.