Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance a cikin wata tafiya, sai ya ga wani mutum mutane sun haɗu a kansa alhali an yi masa inuwa saboda zafin rana da tsananin ƙishirwa, sai ya ce: Me ya same shi ? sai suka ce: Mai azimi ne, sai ya ce: Azimi a halin tafiya bai zama daga cikin ayyukan alheri ba, na horeku da rangwamin da Allah Yayi muku.