Sahabbai sun kasance tare da Annabi a wata tafiya tasa, wasunsu basa Azumi wasu kuma suna yi kuma Annabi ya tabbatar da kowa matsayin da yake kai sai suka a wata rana mai zabi don su huta daga wahalar tafiya da zafin rana, yayin da suka sauka a wannan zafin rana, sai masu Azumi suka fara faduwa sabida da zafin rana da kuma kishirwa basu iya aikata komai ba, sai marasa Azumi suka tashi suka kafamusu shema suka shayar da Rakuma kuma suka yi wa Masu Azumi Hidima, to Yayin da Annabi yaga aikinsu da hidimar da suke na iwa Runduna sain ya karfafa musu a kuma ya fadi falalarsu, kuma ya ce: "Masu Buda baki sun tafi da lada