Abu Al-dardaa yana bada labari _ Allah yarda da shi- cewa sun futo a lokacin wata tafiya a cikin watan Ramalana, kuma ranar ta kasance mai tsananin zafi ce, har ya kai cewa sabida tsananin afinta dayan su yana dora hannunsa a kansa don ya kare rana mai tsanani, kuma duka cikinsu babu Mai Azumi sai Annabi -Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi , da kuma Abdullahi Dan Rawaha Al-ansari - Allah ya yarda da shi hakika su biyun sun jure tsananin kuma sunyi Azumin wanda wannan yana nuna halascin yin Aumi a tafiya duk da wahalar da take ciki wacce batakai matsayin wacce zata kai hallaka ba .Taisir Al-allam (shafi27) Tabih Al-afham (Mujalladi 3/432) Ta'asisu Al-ahkam3/241).